Bangaren kasa da kasa:Manasa harkokin kudi a Faransa a ranar Talata ce suka shirya wani taron karawa juna ilimi mai lakabin dubi a cikin yanayin saye da sayarwa a ramcen kudu a Musulunci kuma a Turai kuma wannan taro a gudanar da shi ne a birnin Paris babban birnin kasar ta faransa inda yan faransa suka bukaci karfafa bin salon ma'amalar kudi a musulumce.
A Wani rahoto da ta nakalto daga shafin internet na Aljazira Net ,cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa labarin cewa: masana a kasar Faransa a wannan taron karawa juna ilimi sun bukaci gwamnatin wannan kasa da ta yi aiki da tajrubar da bankokin msulunci suke da ita da kuma kaddamar da shirin cinike da saye da sayarwa da bada bashi irin na msulumci. Wadannan masana sun bayna cewa hanyar magance wannan matsalar tattalin arziki da Faransa da sauran kasashen Turai ke fuskanta ita ce amfani da salon da tsarin kudi na musulunci da kuma bawa bankokin kasar wannan dama. Har ila yau wannan taro ya jaddada cewa gwamnatin Faransa na iyawa ta maida tsarin bankokinta su yi daidai da na musulunci da hukumce-hukumcen addini kuma za su ja hankulan masu saka hannayen jari musulmi da karawa Faransa karfin tattalin arziki.
362586