Cibiyar koyar da Alku'ani a Iran Iqna ta jiyo daga jaridun cikin gida a Sudan cewa an gudanar da wani gagaramin taro kan muhimmancin fassara Alkur'ani mai girma a cikin Harsunan cikin gida a nahiyar Afrika domin haka zai taimaka matka wajen fahimtar da al'ummar Afrika sanin Alkur'ani a cikin Yarensu .Kuma hakan zai taimaka masu matuka fahimtar Addini cikin sauki babu wata takurawa ta koyan larabci kafin su san Alkur'ani.Da dama daga cikin mahalarta wannan taro sun gamsu da bayanai dam asana daga kasashe da yankuna daban-daban suka yi kan wannan manufa ta fassara Alkur'ani a cikin harsunan Afrika da cewa wannan wani aiki da kokari ne ya kamata a ce tun tuni an yi amma yanzu guri bai kure ba domin amfanin abu za a duba kuma mutanan nahiyar Afrika al'umma ce da ta yi ammana da koyarwa ta Alkur'ani da karbar irin wannan kokari hannu bibiyu a kowane lokaci da yanayi.
362461