IQNA

Koyar Da Hukumce-hukumcen Alkur'ani Ga Muballige A Kasashe Da Ba Na Musulmi Ba

Bangare kasa da kasa:a ranar talata ce a hadaddiyar daular Larabawa aka fara bawa masu tabligi da wa'azi musulmi a kasashe dab a na musulmi horo na kasa da kasa kan sanin hukumce-hukumcen Alkur'ani da tilawa da tajiwidin Alkur'ani
Cibiyar koyar da Alkur'ani a IranIqna bayan ta nakalto daga Jaridar Albayan da ake bugawa a Hadaddiyar Daular Larabawa ta watsa rahoton cewa: wannan horo a wannan karo za a bawa koyar da hukumce-hukumce na Alkur'ani da Hadisan manzon Allah (SWA) muhimmanci inda masu tabligi 120 da yawancinsu suka za su gudanar da aikinsu na tabligi a kasashe dab a na musulmi ba kuma za su share makonni biyu ana bas u wannan horo. Ibrahim Hamadi shugaban muassasar koyar da Alkur'ani da Hadisan Manzon Allah (SWA) a hadiddiyar daular larabawa ya bayyana cewa: a wannan karo manyan malummai ne aka ware da za su bawa masu tabligi a kasashen da ba na musulmi ba horo domin sanin makamar aiki da abubuwan da suke jiransu a irin wadannan kasashe. Tare da jan hankali mahalarta wannan horo da cewa ;mafi muhimmanci shi ne aiki da abin da suka koya a gurin wannan horo.

362561