Bangaren Kasa da kasa: Taron cika shekara daya da shahadar Imad Mugniya da aka bawa sunan Raudar Rudwan ta biyu kuma madogarar al'umma mai juyayin shahadar Imad Mugniya ce ta shirya tare da halartar mutane daban-daban ,jami'an soji da na gwamnati da waikilan kungiyar Hizbullah a Tehran kuma an gudanar da wannan taro ne a nan Tehran a ranar alhamisda ta gabata a masallacin Imam Sadik (AS) da ke dandalin Palsdinu.
A gurin wannan taro cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta bada labarin cewa; a wannan taro Ali Za'ir sakataren kula da al'adu a ofishin kungiyar Hizbullah a Tehran a lokacin da yake gabatar da jawabi ya fara ne da murna da zagayowar nasarar juyin juya halin musulunci a Iran da cwa: wannan nasara ta juyi ta koyar da masu rauni hanyar gwagwarmaya da masu danniya da zalumci .Ya kara da cewa: Imad Mugniya ya fahimci hakika da hanyar gaskiya ta juyin musulunci da ta Imam Khomeini ® day a koyar da shi yakar zalumci da azzalumai .Shi kuwa shugaban ofishin gidan talbijin na almanar a nan Tehran ya yi nuni ne da ruhin yakar ma'abuta girman kai da danniya da cewa Mugniya yanada ruhi mai karfi da daukaka day a karfafa masa wajen yaka da karya makiya HKI da har abada ba za su manta shi ba kuma ya za abin koyi ga al'umma da sadaukar da raid a rayuwarsa.
363169