IQNA

Maroko Za Ta Karbi Bakumcin Taron Isra'ila Mai Kisan Kiyashi Da Tabka Leifukan Yaki

13:54 - February 14, 2009
Lambar Labari: 1744005
Bangaren kasa da kasa:taro kan Haramtaciyar Kasar Isra'ila wadda ta tabka leifukan yaki da kisan kiyashi kuma burin wannan taro shi ne ilmantarwa karkashin hukumar al'adu da ilimi ta musulumci tare da hadin guiwar hukumomin Palasdina da na kasa da kasa masu rajin kare hakkin dan adam kuma aranekun asabar da lahadi ne za a gudanar da wannan taro.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce bayan ta nakalto daga ISESCO ta watsa labarin cewa: wakilan kungiyoyin kasa da kasa masu rajin kare hakkin dan adam da masana na kasa da kasa kungiyoyin wakilai na kasa da kasa da kum wasu shaidun gain da ido kan ta'addancin Haramtacciyar kasar Isra'ila kan yankin Zirin Gaza suna daga cikin wadanda za su halarci gurin wannan taro.Mahalarta wannan taro za su yi dubi da bayani dalla-dalla kan hare-haren ta'addancin gwamnatin HKI kan al'ummar Palsdinu fararen hula a mummunan niyar kawar da al'ummar Palsdinu daga doran kasa kuma mahalarta taro za su yi kokarin ganin sun kare hakkokin al'ummar Palsdinu da shigar da karar shugabannin Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa mai hukumta leifukan yaki.Abdul Aaziz Usman babban sakataren kungiyar ta ISESCO zai gabatar da jawabi yadda za magance wannan babbar matsala da Palasdinawa ke fuskanta.

363364

captcha