IQNA

An Hana Dan Majalisar Dokokin Holand Sabka A Filin Jirangen Sama Na London

Bangaren kasa da kasa: Giret Wildrez dan majalisar dokoki a Holand mai tsananin kiyayya da addinin musulunci wanda ya yi fim din Fitina ta cin Zarafin musulunci an kama shi a filin sabkar jirage na Hitro a birnin London tare da maida shi kasarsa ta Holand.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: kakakin ma'aikatar cikin gida a Britaniya ya sanar da labarin cewa: bayan da gwamnatin Britaniya ta hana wannan dan majalisa Vizas ta izinin shiga kasar ta Britaniya tare da yi masa kashedin abin da zai iya faru na rashin tsaro da zarar ta sa kafarsa a wannan kasa amma duk da haka wannan dan majalisa na kasar Holand mai mummunan mugun ra'ayi ya yi watsi da matsayin gwamnatin Britaniya inda ya sabka afilin sabkar jirage na Hitro.Ya kara da cewa: karkashin dokokin kasar Britaniya duk wanda ba yada izini ya shiga kasar yan sanda za su kama shi da maida shi kasarsa don haka aka maida shi kasarsa ta Holand . sai dai gwamnatin Holand ta nuna takaicinta dad a kama dan majalisar dokokin kasarta. Duk da cewaya samu gayyata don halartar wata kasuwar baje kolin fina-finai a kasar ta Britaniya amma an yi watsi dab a shi Vizas saboda matakan tsaro da shaida masa haka cewa tsaro da kwaciyar hankali a tsakanin al'umma shi ne ya fi komi ga gwamnatin Britaniya.

363339