Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan ta nakalto daga jaridar aljazira ta kasar saudiya ta watsa rahoton cewa: wannan taro za a gudanar da shi ne tare da halartar wakilai 110 mahardata Alkur'ani daga kasashen musulmi karkashin sa idon Muhamda bin Fahad bin Abdul Aziz ali Saudiya amirin yankin Sharafain na Saudiya kuma za a samu halartar Salih bin Abdul Aziz alsheikh ministan addini a Saudiya kuma shugaban komitin koli na karatul alkur'ani da harda a wannan kasa.bada kariya ga tsaron tunani da na ruhi da zamantakewa,hardar Alkur'ani a tsakanin Iyali,hardar alkur'ani tsar one ga al'umma ,karanta alkur'ani tsaro da kwaciyar hankali suna daga cikin abubuwan da wannan taro za a tattauna da yin nazari a ciki tare da gabatar da makaloli.
363388