Kamafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamkamfanin dillancin labaran ( Daghestan Ria) cewa wannan mujallar wadda za ta kasance a cikin shafuka 50 za a fara yada tan an ba da jimawa ba.
An shirya cewa za a fara yada mujallar ne a cikin birnan Moscow, da Sent Petersburg, da Samara, daga bisani kuma za a yada a cikin jamhuriyoyin Tatatar, da Dagistan da sauran kasashen yankin kamar su Ukraine, Belarus, Azarbaijan da dai sauransu.
Daga cikin abubuwan da mujallar za ta kunsa har da sha'anin iyali, motsa jiki, lokutan shakatawa, sana'ar dinki, tafiye-tafiye, koyon harshen larabci da dai sauransu.
363920