IQNA

An fara Nuna Adawa da bawa Yan Sanda Damar Sanya Kayan Musulunci A Norwei

Bangaren kasa da kasa : gwamnatin Norwei na son canja matsayinta na bawa Yan sanda dammar sanya kasan musulunci a fadin kasar.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Islam online ta watsa labarin cewa: Ibrahim Balkiyani shugaban hadin guiwar kungiyoyin musulmi a Norwei a ranar juma ce da ta gabata ya bayyana cewa: wannan mataki da gwamnati ta doka na canja matsayinta abin bakin ciki ne ga musulmin wannan kasa da cewa; wannan mataki ya kawo matsala da cikas ga mata da ke son sanya kayan musulunci a lokacin da suke gudanar da aikinsu nay an sanda wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar kuma wannan zai hana mata yan tsuraru a kasar da ke son bada gudummuwar a ayyukan yan sanda. Kafin wannan wata mata ce yar asalin Aljeriya ta gabatar da bukatarta a gaban kotu kan bat a dammar sanya Hijabi a lokacin da take gudanar da aikinta kuma ta ke sanye da hijabin inda ma'aikatar shari'a a kasar ta amince da wannan bukata cewa a dokokin kasar babu dokar tamtance kayan da mutum zai sanya kuma kayan yan sandan kasar za a canja da zai yi dai dai da kayan musulunci kuma shugaban yan sandan wannan kasa ya amince da wannan mataki amma masu adawa da masu mara masu baya ya sa kotu ta canja matsayinta.

363790