IQNA

Fara gasar kur'ani da hadisi a birnin Doha na kasar Qatar

16:28 - February 16, 2009
Lambar Labari: 1744721
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da gasar karatun alku'ani da hadisi a birnin Doha na kasar Qatar a babban filin wasannin Algurafah da ke tsakiyar birnin.
Cibiyar kula da harkokin alku'ani ta Iran Ikna ta nakalto daga jaridar kasar Qatar Al-rayah cewa; wannan gasa an fara gudanar da ita ne a karkashin kulawar hukumar kula da harkokin matasa ta kasar, kuma matasa masu sha'awar karatun alkur'ani daga ko'ina cikin fadin kasar suna halartar taron gasar.

Wasu daga cikin matasan suna bangaren harda ne, wasu kuma kira'a, yayin da wasu suna banagaren hardar hadisai ne, bayanain ya kara da cewa wasu daga cikin 'yan kasashen waje da suke zaune a kasar ma suna halartar gasar.

364424



captcha