IQNA

A'immat Ahlul-Bait (AS) su ne fassararren alkur'ani.

16:27 - February 16, 2009
Lambar Labari: 1744724
Bangaren Nazari: Bincike kan hanyoyin samun sahihan fassarorin alku'ani na asali ya tabbatar da cewa; sirar A'immat –Ahlul bait na tattare ne da hakikanin fassarar alku'ani ta asali, inda rayuwarsu take fassara ma'anar alkur'ani a aikace.
A binciken da bangaren nazari na cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Iran Ikna ya gudanar kan ma'anar fassarar alkur'ani sahihiya a cikin littafan tarihi da makalolin masana, ya fitar da sakamako da ke nuni da cewa rayuwar A'immah na tattare da hakikinin fassara ta ma'anonin alkur'ani, wanda hakan yake aikace a cikin dukkanin ayyukan rayuwarsu, da hakan ya hada da maganganunsu, sulukinsu, ayyukansu nay au da kullum, mu'amala, rayuwar zamantakewa, tafiyar da jama'a, hukunci da warware matsalolin al'umma, da dai dukkanin abin da yake damfare da rayuwarsu mai albarka.

Da dama daga cikin masana sun rubuta makaloli musamman kan Imam Ali (AS) yadda rayuwarsa da maganganunsa suke fassara alkur'ani ta fuskacin ma'ana da aiki.


364341
captcha