Bangaren kula da ayyukan da suka shafi Kur'ani: Shugaban bangaren da ke kula ayyukan isar da sakon alkur'ani a kasashen duniya cibiyar (Dar Al-kur'an) ta Iran, ya bayyana cewa ana samun ci gaba a ayyukansu a kasashen daban-daban, amma hakan na bukatar zage damtse.
A Wata hira ta musamman da cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Iran Ikna ta gudanar tare da (Daud Tak Falah) ya bayyana cewa suna aikewa da mutane zuwa kasashen duniya domin isar da sakon alkur'ani da wayar da kan mutane kana bin da alkur'ani ke koyarwa, kuma ana samun ci gaba matuka, amma kuma a lokaci guda akwai bukatar wani shiri na musamman domin agazawa wannan aiki ta yadda zai dore. Ya ce akwai abubuwa da dama da wannan aiki ke bukata, domin kuwa aiki ne yawa, kuma yana bukatar kyakkyawan shiri, kamar bayar da horo ga mutanen da ake aikkewa, da kuma kara samara da wadatattun kayan da suke gudanar da ayyukansu da su.
363437