Bangaren Siyasa: shugaban majalisar shawarar musulunci na Iran bayan tattaunawar da ya yi ta waya da shugabannin majalisun dokokin Sudan da Niger ya bada labarin gudanar da taron majalisun musulunci ba da jimawa ba kan Palasdinu a nan Tehran inda za a samu halartar shugabannin masalisun kasashen musulmi.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ce bayan ta nakalto daga ofishin da ke kula da watsa labarai na majalisar shawarar musulunci a Iran ta watsa rahoton cewa:Ali Larjani a wannan tattaunawa ya yi nuni da yanayin da yankin gabas ta tsakiya yake ciki kuma yanayin Palsdinu ya fi muni da muhimmanci don haka ya bukaci kasashen musulmi da cewa;akwai bukatar a ci gaba da taimakawa al'ummar Palasdinu ta dukan bangarori da zai taimaka masu fita daga cikin wannan kangi. Ya kuma sanar da gudanar da wani taron majalisun kasashen musulunci a Iran kan Palasdinu nan bad a jimawa ba. A ci baga da tattaunawar da takwarorinsa na Sudan da Niger Ahmad Ibrahim Tahir da Mahamman Usman na Niger Larjani ya jaddada masu muhimmanci taimakawa Palasdinawa a daidai wannan lokaci.Ibrahim Tahir ya bayyana cewa dole dukan kasashen musulmi su taimakawa al'ummar Palasdinu ta dukan karfin da suke da shi.Shi kuwa Mahamman Usman shugaban majalisar dokokin Niger ya bayyana cewa: a yanayin da ake ciki a yau ya zama wajibi kasashen musulmi su fi maida hankali kan lamarin Palasdinu kuma majalisun kasashen musulmi su maida hankalinsu kacokam kan Palasdinu.
364371