Bangaren Siyasa:Shugaban majalisar shawara ta Iran a hirar da ya yi ta wayar Tarho da takwarorinsa na kasashen Suriya da labanon ya shaida masu wajibcin taimakawa al'ummar Palasdinu kuma yanayin da al'ummar Palasdinu ke rayuwa a Gaza ya damu kasashen musulmi dole a doki matakin da ya dace.
Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta majalisar shawarar musulunci a Iran,Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa labarin cewa: a ranar lahadi ne Ali Larjani shugaban majalisar shawarar musulunci a Iran ya tattauna da takwarorinsa na kasashen Surya da labanon.A wannan tattaunawa ya yi nuni da canjin baya-bayan nan da aka samu a Palasdinu na harin ta'addancin HKI kan al'ummar Gaza da nuna masu rashin tausayi da cewa: yanayin rayuwar al'ummar Palasdinu a Gaza ya munana matuka gaya kuma ba za a iya hakuri da haka ba domin al'ummar yanki na ci gaba da rayuwa cikin killacewa ya kuma bukaci kasashen musulmin da su taimakawa wannan al'umma cikin gaggauwa ya kuma shaida masu ce Iran nada niyar daukan dawainiyar gudanar da taron shugabannin kasashen musulmi kan Palasdinu a nan Tehran a tsakiyar wata mai kamawa ya kuma gayyace su da su halarci wannan taro sun kuma jinjina masa da wannan tunani da kokari na taimakawa al'ummar Palasdinu. Daga karshe ya tabo maganar yadda gwamnatin HKI ke hana duk wani taimako isa ga al'ummar Palasdinu duk da halin da suke ciki.
364490