IQNA

Gudanar Da Taron Cika Kwanaki Arba'in Da Shahadar Imam Huseini (AS) A Pakistan

11:59 - February 16, 2009
Lambar Labari: 1744759
Bangaren Siyasa da zamantakewa:An gudanar da taron juyayin cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Huseini (AS) jikan Manzon Allah (SWA kuma a duk cibiyoyin al'adu na Iran da ke kasar Pakistan ne aka gudanar a daren ranar Lahadi kuma da misalign karfe goma agogon kasar a birnin Islam Abad.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a iran Iqna ce ta jiyo daga ofishin kula da al'adu na Iran a kasar ta Pakistan cewa a lokacin gudanar da wannan taron juyayin tunawa da cika kwanaki arba'in da shahadar imam Huseini (AS) an samu halarta da jawabi daga Murtada Ali Sahibul Fusul shugaban ofishin al'adu na Iran a Islam abad inda ya bayyana muhimmancin raya ranekun ashura da wannan rana ta arba'in domin zai kara fadakar da jama'a zalumcin da aka aiwatar kan wannan bawon Allah day a sadaukar da rayuwarsa don kare addinin musulunci da musulmi haka kuma zai tunatar dam u zalumcin da ake aikatawa kan sauran bayun Allah a wannan duniya tam u. Kuma a gurin wannan taro an samu halartar Iraniyawa masu yawa da ke zaune a wannan kasa ta Pakistan kuma sauran yan Shi'a a Pakistan.

364647

captcha