IQNA

Cibiyar Ikna ta samu gagarumin ci gaba wajen gudanar ayyukan na alkur'ani

10:35 - February 17, 2009
Lambar Labari: 1744831
Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da harkokin kur'ani ta Ikna, tare da hadin gwiwa da hukumar kula da al'adu da dangantakar kasashen musulmi, da kuma jamia'ar Mostafa, ta cimma nasarar gudanar da ayyukanta da dama.
Cibiyar kula da ayyukan na alkur'ani a Iran ikna ta habarta cewa; an gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin mambobin cibiyar da kuma na hukumar kula da al'adu da dangantakar kasashen musulmi, da kuma na jamia'ar Mostafa, dangane da yadda bangarorin uku za su ci gaba da yin aiki tare ta fuskacin bunkasa al'adu na musulunci, da kuma ayyuka da suka shafi yada fahimtar alkur'ani tsakanin al'ummomin duniya.

Kamar yadda bangarorin uku suka yi dubi ga ayyukan da suka gudanar na hadin gwiwa tsakaninsu a lokutan baya, da kuma sakamakon da hakan ya bayar, inda bayanin ya yi nuni da cewa dukkanin bangarorin sun gamsu da sakamakon ayyukan.

364841

captcha