Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Alarab online) cewa; mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi larabawa Abdulazim Almagribi ya fadi yau a wajen taron birnin Ribat, da ke tattauna ayyuakan kisan kiyashi da yahudawan sahyuniya suka yi kan al'ummar Gaza, cewa a hare-haren da sojin yahudawan sahyuniyan suka kai kan Gaza na tsawon kwanaki 22, sun rushed a dama daga cikin cibiyoyin ilimi da al'adu, da suka hada da makarantu da jami'oi, wanda hakan ya cancanci a gurfanar da shugabannin gwamnatin yahudawan a gaban kotun manyan laifuka ta duniya domin fuskantar shari'a.
364631