Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kafar yada labarai ta BBC cewa; tawagar masu gudanar ayyukan jin kai ta London ta kama hanyar Gaza, domin kai taimako na kayayyaki da aka kaddara kudinsu da Pound miliyan daya. Daga cikin kayayyakin kuwa hard a motoci 100, da suka hada da na kashe gobara, da na daukar marassa lafiya, da kuma motocin daukar kaya, a cikin kayan kuma akwai kayan abinci, da magunguna, tufafi, barguna,da dai sauransu.
George Galawi wani dan majalisa ne a kasar Birtaniya, wanda ya yaba da kokarin da masu bayar da agajin suka yi, inda ya bayyana cewa; taimakon al'ummar gaza taimako ne ga 'yan adamtaka.
364544