IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Kusanto Da Fahimtar Mazhabobin Musulunci A Kasar Tunusia

Bangaren kasa da kasa: An bude taron kusanto da fahimtar mazhabobin Musulunci a karo na biyu a kasar Tunusia, da nufin kara hada kan musulmi domin fahimtar banbancin mazhabobinsu wadanda dukkaninsu sun ginu ne bisa manufar addini.
Cibiyar kula da harkokin alkurani ta Ikna, ta nakalto daga kafar yada labarai ta Allafrica cewa; ma'ikatar kula da mazhabobin Musulunci ta kasar Tunusia ce ta shirya taron na hadin gwiwa tsakaninta da ma'aikatar kula da harokin addini ta kasar Masar, inda taron ke samun halarta masana daga kasashen biyu, da suka hada malam jami'oi gami da shugabannin kungiyoyin addinin Musulunci, musamman daga kasashen larabawan arewacin Afirka. Babbar manufar taron dai ita ce kawar da rashin fahimtar juna tsakanin musulmi mabiya mazhabobi daban-daban, tare da hada kansu kan fahimta guda taddinin Musulunci, tare da girmama ra'ayin kowane bangare daga cikin mazhabobi.

365185