Bangaren kasa da kasa: Da dama daga cikin al'ummomin Birtaniya musulmi da wadanda ba musulmi ba, sun nuna gamsuwarsu da tsarin inshora na wani kamfanin musulmin kasar mai suna (Salam Halal)
Cibiyar kula harkokin alkur'ani ta Ikna, ta nakalto daga shafin internet (Islamonline) cewa; kamfanin Salam Halal shi ne kamfanin inshora na farko da musulmin Birtaniya suke da shi, kuma ya fara gudanar da ayyukansa ne a cikin wannan shekara ta miladiyya, bayanin ya ce kamfanin yana amfani da tsarin Musulunci ce wajen gudanar da ayyukansa, amma kuma a lokaci guda musulmi da wadanda ba musulmi ba ne a kasar Birtaniya duk sun nuna gamsuwarsu da yadda kamfanin ke tsara ayyukansa tare da gudanar da su, duk kuwa da masaniyar da suke da ita kan cewa kamfani ne na musulmi da ke kokarin kamanta koyarwar addininsu a cikin ayyukan kamfanin.
365172