IQNA

Masana Sun Karfafa Wajabcin Kyautata Dangantaka Tsakanin Addinai

14:19 - February 18, 2009
Lambar Labari: 1745648
Bangaren Kasa da kasa:Masanan da suka halarci taron Amurka da duniyar musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, sun jaddada wajabcin kyautata danganta da fahimtar juna tsakanin addinai na duniya.
Cibiyar kula da harkokin kur'ani ta Ikna ta nakalto daga jaridar (al-sharq) ta kasar Qatar cewa; a cikin bayanin bayan taron da mahalarta taron suka fitar, sun bayyana cewa wajibi ne dukkanin bangarorin addinai su girmama junansu, tare da kiyaye adalci a duniya, tare da gudanr da tattaunawa a kan kowane irin lamari domin kawar sabani da rashin fahimta, musamman tsakanin Amurka da duniyar musulmi, da hakan ya hada da batun dangantakar wasun kasashen musulmi da Amurka kamar Iran da Afganistan, inda mahalarta taron suka jaddada wajabcin warware takaddama tsakanin Amurka da al'ummomin wadannan kasashe biyu. Kamar yadda suka jadda cewa ya kamata a aikace ne daga bayan kammala taron nasu, wanda shi ne irinsa da aka gudanar a karo na shida.

365198

captcha