Bangare na kasa da kasa: Sarkin Kasar saudiyya Abdallah Bin Abdulaziz ya bukaci da a baiwa mabiya mazhabar shi'a tabbataccen wakilci a majalisar dokokin kasar, inda yanzu haka sun samu wakilci tabbatacce a majalisar.
Cibiyar kula harkokin alkur'ani ta Ikna, ta nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya na (Rasid) cewa; a kokarin da sarkin saudiyya ken a yi gyaran fuska ga yadda ake tafiyar da harkokin mulkin kasar, ya bayar da umurnin bayar da dama ga mabiya mazhabar shi'a na kasar da su shiga cikin majalisar dokokin kasar, domin bayyana matsayinsu kan lamurra da kuma neman hakkokinsu a hukumance a matsayin na 'yan kasa kamar sauran 'yan kasa mabiya sunna.
365315