IQNA

kaddamar da Littafi Kan Musulunci Da Alkur'ani a Farasan

14:04 - February 19, 2009
Lambar Labari: 1746035
Bangaren Al'adu da Kwarewa: an kaddamar da litattafai guda goma sha biyu da suka shafi manzon Allah (SWA) Nahajul Balaga ,Imam Huseini (AS) da kuma Alkur'ani mai girma a faransa.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Ikna cewa bayan ta nakalto daga hukumar yada al'adun Iran a Faransa ta bayyana cewa: wadannan litattafai da aka kaddamar sun shafi sani na hakika kan manzon Allah (swa) da Sharif Muhammad Ali Haidara ya rubuta ,kan kungiyar Hizbull a matsayin tajrubar zamani mai zuwa da Sheikh Na'im Kasim ya rubuta sai kuma Sirril Salla da Imam Khomeini ® ya rubuta da kuma littafin tasirin da dalilan juyin Imam Huseini (AS) da Shahid Mutahari ya rubuta kuma dukansu an tarjama zuwa harshen Faransanci.Bugu da kari akwai sauran litattafai da aka kaddamar da suka kumshi tarihi da sirar manzon Allah (SW) da Said Husein Nasri ya rubuta da littafin Mahdi Alkalin Duniya da Ayatullah Amini ya rubuta da hadisai arba'in na Imam Khomeini da kuma Risalatul hukuk da imam Sajjad (AS) ya yi bayani .

366103

captcha