Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Washington Post) cewa; a lokacin da take gabatar da wata lacca a jami'ar Tokyo a kasar Japan a ranar Talatar da ta gabata, Helary Clinton ta bayyana cewa Amurka za ta ci gaba kokarin kyautata danganatakarta da kasashen musulmi, domin kawo karshen rashin fahimtar juna da ke akwai tsakanin duniyar musulmi da Amurka. Ta kara da cewa; a matsayinta na kirista ta san cewa akwai kiristocin da aka tafka tabargaza da sunan addini, amma hakan ba yana wakiltar addinin kiristanci ba ne, haka nan ma musulmin da suke aikata ayyukan wuce goda da iri da sunan addinin musulunci ta san ba suna wakiltar addini musulunci ba ne.
365864