Bangaren kasa da kasa: Babbar Majami'ar Qibti ta kasar Masar ta yi kakkausar kan Haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da cin zarafin Annabi Isa (AS) da Maryam (AS) da ta yi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Alwatan) ta kasar Saudiyya cewa; majami'ar Qibti ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta bayyana cewa; cin zarafin annabin Isa da Maryam (AS) daya ne daga cikin munanan ayyukan Isra'ila. Bayanin ya kara da cewa al'ummar da ke kwace kasa, tare da yin amfani da muggan makamai da aka haramta a duniya wajen yin kisan kare dangi kan kanan yara da mata, tare da rushe cibiyoyin ilimi, baa bin mamaki ba ne don sun wulakanta addinan da aka safkar daga sama.
366803