IQNA

Wasu Malaman Jami'a A Birtaniya Ba Su Amince Da Gudanar Da Kasuwar Baje Kolin Isra'ila A Kasar Ba

8:41 - February 21, 2009
Lambar Labari: 1746358
Bangaren kasa da kasa: Wasu daga cikin malaman jami'a a kasar Birtaniya sun ce ba su amince da gudanar da kasuwar baje koli kan harkokin ilimin jami'a da Isra'la za ta yi a kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sana cewa; sama da malaman jami'a 380 ne a kasar Birtaniya suka suka sanya hannu kan wata takarda, domin nuna rashin goyon bayansu ga kasuwar baje koli da Haramtacciyar kasar Isra'ila za ta gudanar a jami'oin Landan da Manchester, kan harkokin ilimin jami'a, da hakan ya hada da kayayyakin karatun dangin littafai da abubuwan rubutu da dai sauransu. Malaman jami'ar sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne domin nuna takaicinsu kan kisan kiyashin da Isra'ila ta yi kan al'ummar Gaza.

366734

captcha