IQNA

Za A Bude Sabon Ofishin Kungiyar OIC A Kasar Iraki

8:40 - February 21, 2009
Lambar Labari: 1746359
Bangaren kasa da kasa: A ranar Litinin mai zuwa ce kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC za ta bude sabon ofishinta a birnin Bagdaza na kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-sabah) ta kasar Iraki cewa; a ranar Litinin mai zuwa ce sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmal Al-ddin Aglo zai jagoranci bude sabon reshen kungiyar a birnin Bagadaza, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da zai kai wata ziyara a hukumance a kasar ta Iraki. Bayanin yakara da cewa babbar manufar bude wannan sabon ofishi ita ce samara da hanyoyi da kungiyar ta OIC za ta taimaka ma al'ummar kasar Iraki kai tsaye.


366732


captcha