Kamfanin dilanncin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sana cewa; a jiya ne gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya ta fitar wani bayani, da a cikinsa ta zargi Haramtacciyar Kasar Isra'ila da aikata laifuka na cin zarafin dan adam da suka yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, a lokacin da ta kai hare-hare kan al'ummar gaza da bayan kai harin, domin kuwa har yanzu tana ci gaba da take hakkokin al'ummar yankin marassa kariya.
A banagare guda kuma bayanin ya soki gwamnatin Masar, kan ci gaba da rufe mashigar Rafah da take yi, wanda hakan ya kara jefa al'ummar gaza cikin mawuyacin hali.
366694