IQNA

Samun Masallatan Juma'a Na Daga Cikin Siffofin Biranan Musulmi

Bangare na kasa da kasa: Samun masallatai a cikin birane musamman masallatan Juma'a, wadanda su ne manyan wuraren ibadar musulmi, hakan na nuni ne da tasirin addinin musulunci a cikin wadannan yankuna.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani zama da aka gudanar a babban ginin ofishin kula da ayyuka na alkur'ani da kuma al'adun musulunci a birnin Tehran, babban daraktan bangaren kula da binke na jami'ar AZAD ISLAMI (Hossein Soltan Zadeh) ya bayyana cewa; daya daga cikin muhimman abubuwan da za a yi la'akari da su wajen gano dangantar yankuna ko mutanen birane da addini musulunci, sun hada da samun masallatai a cikin biranansu, musamman ma masallantan juma'a, wadanda su ne manyan cibiyoyin ayyukan ibada ga musulmi.

366200