Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islamonline) cewa; 'yan majalisar na Amurka biyu wato Brain Beard da kuma Ket Aleson, sun bayyana matukar damuwarsu dangane da yadda suka samu al'ummar Gaza, da kuma irin matsanancin halin rayuwa da suke ciki, sakamakon hare-haren kare dangi da Isra'ila ta kai kansu, sun bayyana cewa ci gaba da hana kai taimakon gaggawa ga al'ummar yankin da Isra'ila ke yi, bayan ta rushe dubban gidaje tare da kashe mutanesama da dubu daya, da kuma jikkata wasu dubbai, hakan ya yi hannun riga da dokoki na kasa da kasa. 'Yan majalisar biyu na Amurka sun nuna matukar tausayinsu ga al'ummar gaza, musamman kananan yara da suka rasa iyayaensu, da mata da suka rasa mazajensu samakon yakin na Isra'ila.
366730