Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-watan ) ta kasar saudiyya cewa;gwamnatin Argentina ta baiwa malamin kiristancin dan asalin kasar Birtaniya Richard Willianson wa'adin kwanaki 10 da ya bar kasarta, sakamakon musunta faruwar holocost da ya yi, inda ya bayyana cewa babu wani kisan kiyashi da aka yi kan yahudawa da ya yi sanadiyar mutuwar kimanin miliyan 6 daga cikinsu a Jamus, ya ce yahudawan da suka mustu ba su wuce 300,000 ba, ba miliyan 6 kamar yadda ake ta yayatawa ba. Furucin nasa ya fsukanci kakkausar suka daga Haramtacciyar kasar Isra'ila da ma kasashen da suke daure mata gindi, da ma wasu daga cikin jagororin mabiya addinin kirista, da suka hada da paparoma Benedict na goma sha shida.
367128