Bangaren kasa da kasa: Jami'an tasron kasar saudiyya sun yi awon gaba da wasu masu gudanar ziyara a makabartar Bakia da ke birnin Madina, bayan da suka bukaci masu ziyara da su bar makabartar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Okaz) ta kasar saudiyya cewa; masu gudanar da ziyara a makabartar Bakia da ke birnin Madina sama da 500 ne suka taru, inda jami'an tsaron kasar Saudiyya a cikin kayan sarki suka hana gudanar da ayyukan ziyararsu, kuma suka bukaci kowa day a bar wuri bayan sun wulakanta da dama daga cikin masu ziyarar da suka fito daga kasashen duniya daban-daban, daga bisani kuma suka kame wasu daga cikin masu gudanar da ayyukan ziyara a makabartar wadda aka rufe iyalan gidan manzon Allah da wasu sahabbai a cikinta. Wannan dai ba shi karo na farko da jami'an tsaron kasar Saudiyya ke wulakanta masu gudanar da ayyukan ibada a wurare masu tsarki da ke kasar ba.
366997