IQNA

Tarayyar Turai Ta Yi Alladawai Da Gina Matsugunnan Yahudawa A Yankunan Palastinawa

13:01 - February 22, 2009
Lambar Labari: 1746920
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi kakkausar kan ci gaba da gina matsugunnan yahudawa da Isra'ila ke yi a cikin yankunan Palastinawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; a cikin bayanin da kungiyar tarayyar turan ta fitar, ta kirayi Isra'ila da ta sake yin nazari kan ci gaba da gina matsugunnan da take yi a cikin yankunan Palastinawa, domin kuwa ci gaba da yin haka ya saba wa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma yin hawan kawara ne a kan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra'ila da Palstinawa wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, kuma hakan zai kawo babban cikas ga duk wata tattaunawar sulhu tsakanin Isra'ila da kuma Palastinawa, kuma mai yuwuwa hakan ya kara mayar da hannun agogo baya ga yunkurin da ake yin a samara da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

367221
captcha