IQNA

Cibiyar Yada Musulunci A Washington Ta Watsa Bayanai Kan WAQF A Shafin Internet

Bangaren Internet: Sashen da ke kula da al'adu da yada labarai na cibiyar yada koyarwar addinin muslunci a birnin Washington na Amurka, ta yada bayanai kan makon WAQF(kebance wani abu don yin amfani da shi saboda Allah)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa , bayanan da cibiyar ta watsa a shafin nata, sun shafi ranar Waqf, bayanai kan ma'anar waqf, da wafq din da manzon Allah (SAW) ya yi a lokacin rayuwarsa mai albarka da kuma iyalan gidansa, da kuma samfuri daga bayanan kan wafq na Imam Ali (AS) da waqf a cikin kur'ani mai tsarki, kuma mahangar tarihi da fikihu kan waqf.
A wani banagaren bayanan kuma an tabo rawar da waqf ke takawa ta fuskacin fadada al'adu da ci gaban musulunci, da ma irin gudunmawar da hakan ke bayarwa wajen gina al'umma da taimaka ma rayuwarsu ta zamantakewa.

367278