IQNA

Matsayin Sallar Noruz A Mahangar Limaman Tsarki (AS)

15:18 - February 22, 2009
Lambar Labari: 1747299
Bangaren manema labarai: Muhammad Sadik Nasir Khalil Abad ya bayyana cewa: duk da cewa Alkur'ani babu wata aya da ta yi Magana kan tushen sallar Noruz amma wasu hadisai da sun jaddada kan sallar Noruz da abubuwan da ta kumsa na tarbiyar musulunci.
Akwai ruwayoyi daga limaman tsarki (AS) kan sallar Noruz da aka nakalto daga Imam sadik (AS) da ke cewa: Ranar Noruz ran ace da Allah madaukakin sarki ya kulla alkawali da bayinsa kar su yiwa shirka da hada shi da waninsa sun bad a imani da manzonninsa da waliyansu.Ranar Noruz ita
ce rana ta farko da rana ke fitowa da haskaka duniya,it ace ranar da jirgin Annabi Nuhu ya isa doran kasa kuma ranar da Allah ya aiko da mala'ika Jibril zuwa gurin manzonsa kuma ranar da Manzo (AS) ya doki Imam Ali (AS) a kafadarsa domin ruguza gumakan da suke Ka'aba kuma ranar da imam Ali (AS) ya ci nasara a yaki da makiyan Nahrawan.

366565
captcha