IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani Ta Kasa A Qatar.

9:23 - February 23, 2009
Lambar Labari: 1747448
Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da gasar hardar kur'ani a karo na 16 a kasar Qatar, a cibiyar (Arwa Bint Abdulmutalib) da ke yankin (Dafna) da ke gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-sharq) da ake bugawa a kasar Qatar cewa; za a fara gudanar da bangare na farko a gasar tare da halartar mutane 1600 daga cikin masu gudanar da gasar, kuma za a kasa su zuwa kashi bakwai. Cibiyar kula da gasar karatun kur'ani ta kasar ta bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar mahardata, da kuma masu karatun kur'ani, ta yadda hakan zai taiamaka wajen bayar himma ga hidimar alkur'ani, ta fuskacin harda da ma kyautata karatunsa.

367626

captcha