Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (SPA) cewa; wannan kwas din an gudanar da shi ne da nufin samara da wasu hanyoyi na isar da sakon addinin musulunci ga al'ummar kasar Argentina, ta hanyar sanar da su manzon musulunci Muhammad (SAW) da kuma irin sakon day a zo ma dan adam da shi, wanda a cewar bayanin sanin manzon Allah zai bayar da damar sanin addininsa. An bayar da kwas din ga wasu daga cikin musulmin kasar da suke sha'awar gudanar da ayyukan isar da sakon addinin musulunci ga sauran al'ummar kasar, daga ciki kuwa hard a limaman masallatai.
367639