IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Rubutun Kur'ani A Kasar saudiyya

9:21 - February 23, 2009
Lambar Labari: 1747451
Bangaren kasa da kasa: Gasar rubutun wani bangare ne na gasar kur'ani da sunnar manzo da bayanai na magabata da ake gudanarwa a karo na bakwai a kasar ta Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar saudiyya (SPA) cewa; wannan shi ne karo na bakwai da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar saudiyya, kuma za a gudanar da gasar a sauran yankuna na kasar, hard a gidajen kaso da ma yankuna na al'ummomi marassa rinjaye a kasar. Bayanin ya kara da cewa a wannan karon gasar za ta shafi wasu bangarori da ba ta saba tabo su, da hakan ya hada da gabatar da wasu ayyukan a internet, da hakan ya hada yin amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen gudanar rubuce-rubucen, wanda kuma hakan sabuwar hanya ce ta zamani.

367723


captcha