Bangaren Raho: Sheikh Muhammad Yazbak daya daga cikin malaman kasar Labanan ya bayyana cewa: al'ummar Labanan na ci gajiyar wilayarsu ga Imam Khomeni ne.
Malamin ya bayyana hakan ne kuwa a lokacin da yake jagorantar wata tawagar mutanen Labanan da ta kai ziyara ga Ayatollah Zanjani. Sheikh Yazbak ya kara da cewa; kafin samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran da dama daga cikin mabiya mazhabar shi'a a kasarLabanan suna cikin wahala dab a misiltuwa, amma albarkacin juyin juya halin musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeni (RA) al'ummar da aka danne a Labanan ta samu 'yancinta, kuma hakan ya yi sanadiyar komawar mutane da dama ga addini da koyarwarsa. A nasa bangaren Ayatollah Zanjani ya jaddada cewa juyin juya halin musulunci Iran na al'ummar duniya ne.
367568