Bangaren kasa da kasa: Wata tawaga daga majalisar tarayyar turai za ta isa Jordan a yau, domin duba irin ayyukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta tafka a Gaza a cikin 'yan lokutan da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Jordan Times) cewa; jami'in da ke kula da harkokin manema labarai a cikin tawagar ya sheda wa manema labarai cewa; wannan tagawa za ta duba irin barnar da Isra'ila ta yi wa al'ummar Gaza ne a cikin kwanaki 22 da ta kwashe tana kai hare-hare kan al'ummar yankin, tare da duba yanayin da gabas ta tsakiya ke ciki bayan kawo karshen yakin.
Jami'in ya kara da cewa, tawagar tasu bayan ta kammala ziyararta a Jordan za ta ziyarci Masar, daga nan kuma za su isa zirin Gaza da Ramallah.
368354