Bangaren kasa da kasa: A daidai lokacin da Hamas ta karyata batun aike wa shugaban Amurka da wasika, a nasa bangaren sabon shugaban Amurkan (Barack Hossein Obama) ya aike wa jagororin Hamas din da wata wasika.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; jami'an Amurka sun bayyana cewa jagororin Hamas ba su san da zaman wasikar da aka aike wa Obama daga bangaren kungiyar ba, ta hanyar Sanata (John Kerry) amma a nasa bangaren shugaban Amurka Barack Obama ya aike wa jagorin Hamas din da wata wasika a hukumance kan su kara masa haske dangane batun wasikar da aka aike masa.
Wasu majiyoyin kungiyar Hamas sun tabbatar da cewa wani jami'I ne a ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Hamas ya rubuta wasikar , amma ba da sunan kungiyar Hamas ba.
367785