IQNA

Gwamnatin Kasar Masar Ta Bude Mashigar ( Rafah )

12:15 - February 24, 2009
Lambar Labari: 1748089
Bangaren kasa da kasa: Jami'an gwamnatin kasar Masar sun bayar da umurnin bude mashigar Rafah, domin bayar da dama ga wasu daruruwan su shiga cikin kasar ta Masar ta wannan mashiga.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AP cewa; daya daga cikin jagororin Hamas (Adel Zourab) ya bayyana cewa; gwamnatin kasar Masar ta amince ta bayar da dama ga wasu dalibai Palastinawa kimanin dari biyar da suke karatu a wajen kasar, ko kuma suke dauke da takardun shedar zama dan kasa na wasu kasashen, da su wuce ta mashigar Rafah, domin bi ta hanyar Masar wajen komawa kasashen da suke karatu ko suke da takardun zama 'yan wadanacan kasashen.
Tun a cikin shekara ta 2007 ce gwamnatin Masar ta rufe mashigar Rafah, inda ta hana Palastinawa shiga cikin kasarta daga zirin Gaza, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin wani mawuyacin hali, musamman bayan da Isra'ila ta killace yanki baki daya.

368250











captcha