IQNA

An Fara Binciken Yadda Za A Kafa Komitin Malumman Palasdinu A Ketare

Bangaren Siyasa da Zamantakewa; Malumman Labanon da takwarorinsu a wasu kasashen larabawa sun fara wani zama a babban birnin kasar Labanon Beirut da zimmar binciken dokokin kafa komitin malumman Palasdinu a ketare.
Reshen cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a iran Ikna da ke Labanon ne ya bada labarin da cewa: a wannan zama sheikh Abdulgani Tamimi ya yi bayani kan burin kafa wannan komiti na malumman palasdinu da ke zaune a ketare da cewa: burin kafa wannan kimiti shi ne fuskantar shirin da yahudawan Sahayoniya suka gabatarwa larabawa kuma hakan zai taimakawa hadin kai a tsakanin Palasdinawa.Ya kara da cewa; kokarin labanon shi ne taimakawa palasdinawa su koma kasarsu tag ado kuma ya jinjinawa kokarin kungiyar kasa da kasa ta kudus da mai bada fatawa a Labanon kan yadda suka himmatu da lamarin palasdinu.Dawud Mustapha shugaban hadin guiwar malumman Palasdinu a Labanon a cikin bayaninsa ya yi nuni da shirin Malummai kan lamarin Palasdinu da cewa: intar da kasar Palasdinu wani abu ne day a wajaba kan al'ummar Palasdinu kuma tushen nauyi da wajibcin ya rataya kan shugabanni da jagororin musulmi.

368106