Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta bada labarin bayan ta nakalto daga cibiyar labarai na Hauza cewa: Husein Asadi sakataren shirye-shirye na wannan gasara karo na sha hudu na Olumpik din Alkur'ani da Hadisai a Jami'ar Almustapha Al'alami ya bayyana cewa tuni suka raba littafai sama da dubu 11 da takardar gayyata a ciki da wajen Iran kan wannan gasa.asadi ya kara da cewa; kuma tuni suka raba karamin littafin nunahanya da bayani kan gasar dubu hudu a ciki da wajen Iran a cibiyoyi da makarantu da ked a alaka da wannan hukuma.har ila yau sun raba litafin da ya kumshi hadisai da Addu'o'I dubu daya sai kuma dubu daya na ayoyi da suke Magana kan lamurra kuma sun raba Alkur'ani dubu daya bugu da kari da wasu dubban littafai da suka shafi kare hakkokin ma'aikata a mahangar Imam Ali (AS) kuma mahardata daga kasashe 65 ne za su samu halartar wannan gasa.
367713