IQNA

Yan Shi'ar Ghana Sun Fara Juyayin Shahadar Imam Rida (AS)

Bangaren Siyasa da Zamantakewa: Yan Shi'a a Ghana za su gudanar da taron juyayin shahadar imam Rida (AS) a ranar Talata a masallacin ma'aikin Allah (SWA) a birnin Accra.
Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga ofishin kula da yada al'adun Iran a Ghana ta watasa rahoton cewa: wannan taro za a gudanar da shi ne tare da gabatar da jawabai da buga kirji tare da halartar Iraniyawa da ke zaune a wannan kasa da ke yammacin Afrika a zauren gudanar da tarurruka na ofishin kula da yada al'adun Iran a Ghana. Kuma Huseini shugaban jami'ar musulunci a Ghana kuma malami a jami'ar yana daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a gurin wannan taro na juyayin shahadar Imam Rida (AS).

367947