Hujjatul Islam (Nasrollah Pormanfar) a cikin wata hira da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce jawo hankulan al'ummomin duniya zuwa ga fahimtar sakon da ke cikin alkur'ani mai tasrki, wanda shi ne shiriya ga talikai baki daya, tare da sanin ma'anonin alkur'ani ta hanyar hadisan manzon Allah.
Ya ce idan aka yi la'akari da yadda fahimtar musulunci da sakon da yake dauke da shi hakan ya yi rauni a tsakanin al'ummomin wasu nahiyoyi na duniya, hakan na nuni ne da wajabcin ci gaba da bin dukkanin hanyoyi da suka sawaka na zamani domin isar da wannan sako mai tsarki.
367968