Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa: a wani bayani da banagaren yada labrai na majalisar shawara ta Iran ya fitar, shugaban majalisar Ali Larijani ya gudanar da wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho tare da shugaban majalisar dokokin kasar BahrainAli bin Saleh Al-saleh, inda suka tattauana muhimman batutuwa da suka shafi dangantakar kasashen biyu, inda Larijani ya jaddada cewa a mtsayin kasashen biyu na makwafta dangantaka za ta ci gaba da kara fadada a tsakaninsu.
A bangare guda kuma sun tabo batun Palastinu da halin da al'ummar Gaza suke ciki sakamakon hare-haren da yahudawan sahyuniya suka kai kansu a 'yan lokutan baya, inda ya bayyana cewa al'ummar gaza na bukatar taimako fiye da sauran lokutan baya.
Ali larijani ya kirayi shugaban majalisar dokokin kasar Bahrain zuwa taron shugabannin majalisun dokoki na kasashen musulmi da za a gudanar nan gaba a birnin Tehran, wanda zai yi dubi kan halin da al'ummar Gaza suke ciki, da kuma irin taimakon da suke bukata.
368212