Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Almuslim) cewa; sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmal Ihsan Oglu ya fitar da wani bayani a yau, da a cikinsa ya yi kakkausar suka kan matakin da Isra'ila take dauka na ci gaba da rushe gidajen palastinawa da ke birnin Quds, tare da mayar da su matsugunnan yahudawa, ya ce wannan mataki ne mai matukar hadari, da ke nufin mayar da birnin Quds mallakin yahudawa kadai, tare da shafe duk wata alamar Musulunci a birnin, da hakan zai iya kaiwa ga rushe masallacin Quds. Ya kara da cewa gina ramuka da yahudawa ke yi karshin masallacin wata manuniya ce kan hakan.
368995