IQNA

Kafa Komitin Shirya Dokoki Kan Tattalin Arziki A Saudiya

13:56 - February 25, 2009
Lambar Labari: 1748563
Bangaren kasa da kasa: Saudiya tana da niyar kafa wani komiti da zai yi dokoki a duk sha'anin day a shafi tattalin arziki.
Cibiyar kula da koyarwa ta Alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Financeislamique ta watsa rahoton cewa: Yusuf Abdullah Alzamil mataimakin shugaban asusun kasa da kasa kan tattalin arziki a Musulunci a saudiya ya bayyana cewa: shugabannin bada lamani a musulunce da asusun kasa da kasa a musuliunce sun tuntubar juna domin samara da wasu dokoki na bai daya a musulunce kafin shekara ta 2010.Ya kara da cewa: wannan komiti nada nauyin bincike da tattalin arziki da dokokin da suka shafi wannan fanni.Wannan mataki dai ya biyo bayan matsalar tattalin arziki da kasashen duniya suke fuskanta ta tabarbarewar tattalin arziki musamman manyan kasashe daga cikinsu.

368869
captcha