IQNA

Komitin Kula Da Buga Alkur'ani A Panjab Sun Galgadi Masu Buda Alkur'ani

13:55 - February 25, 2009
Lambar Labari: 1748566
Bangaren kasa da kasa: Komitin kula da buga Alkur'ani a lardin Panjab na kasar Pakistan sun galgadi masu buga alkur'ani da su rika kiyaye dokokin bugawa da yada Alkur'ani.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa jaridar THE news ta buga labarin cewa; Allama Ahmad Ali Kasuri shugaban komitin masu lura da budawa da kuma yada Alkur'ani a lardin Panjab ya bayyana cewa; dukan takardun da suke amfani da su wajen buga Alkur'ani ba takardu ba ne masu ingaci kuma har ila yau taddawar da suke amfani ba wadda ake bukata b ace don haka a nan da makonni biyu dole sun kyautata aikinsu . ya kara da cewa ba za su ci gaba da amince da irin wannan hali da yin sakaci da lamarin day a shafi bugawa da kuma yada Alkur'ani a kasashen duniya.

368881

captcha